Gwamnatin Kasar Saudiyya ta rufe wasu manyan masallatai bayan an samu cikin masu ibada da suka kamu da cutar korona kamar yadda kafar BBC Hausa ta ruwaito.
Ma’aikatar lamurran addini ta kasar ta ce masallatai biyar ne aka rufe, hudu a Riyadh babban birnin kasar da kuma daya da ke kusa da kan iyaka a yankin arewaci, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya bayyana.
Masallatai kimanin 57 zuwa yanzu Saudiyya ta rufe cikin mako daya, yayin da aka bude 44 daga cikinsu bayan an yi masu feshi da kuma gindaya sharadda ga masallata.
Gwamnatin ta bukaci mutane su kiyaye sharuddan kwayar cutar korona tare da bayar da rahotanni kan duk masallacin da ya saba dokokin.
A rahotannin baya bayan nan dai na nuni da cewar adadin masu kamuwa da cutar ta CORONA na ?aruwa sosai a kasar ta Saudiyya.