Saudiyya Ta Haramta Wa Kasashe Hudu Shiga Kasarta

Saudiyya ta dakatar da jigilar jirage zuwa ƙasashe huɗu da suka haɗa har da maƙwabciyarta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin daƙile bazuwar korona.

Matakin na zuwa ne bayan Saudiyya ta ce ƴan ƙasarta da aka yi wa rigakafin korona na iya tafiya ƙasashen waje bayan ɗage haramcin fita daga ƙasar tsawon shekara ɗaya.

Daular Larabawa musamman birnin Dubai, ya kasance wurin shaƙatawa ga yawancin ƴan Saudiyya.

Sauran ƙasashen da Saudiyya ta hana jigila sun haɗa da Habasha da Vietnam da Afghanistan, kuma matakin zai fara aiki ne ranar Lahadi, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.

Ƴan Saudiyya da suka fito daga ƙasashen za a killace su tsawon mako biyu. Kuma an haramta wa ƴan ƙasar tafiya ƙasashen ba tare da izinin hukumomi ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply