Kasar Saudiyya ta sanar da matakin haramta aurar da mata ‘yan kasa da shekari 18. A sabuwar dokar, Saudiyya ta bayyana cewa duk macen da za’a aurar daga yanzu sai ta kai shekaru 18.
Ministan shari’a na kasar, Sheikh Walid Alsamani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aikewa kotunan kasar.
Jaridar Premium times a cikin wani ruhoto ta bayyana cewa duk cikin mata 7 da aka aurar ana samun akalla 1 da aka mata auren wuri a kasar Saudiyya.
Batun auren wuri ga mata ya zama wani lamari da ake cigaba da tattauna shi a tsakanin kasashen Duniya musanman ƙasashen Musulmi, inda wasu ke ganin tsari ne da shari’a ya bada damar aurar da Mata da wuri, yayin da wasu ke ganin tsarin ya keta ‘yancin Mata.
A bangaren likitanci ma ana samun suka daga sha’anin aurar da Mata da wuri, inda ake kokawa da cewar ana samun wasu cututtuka dake faruwa ga ‘ya’ya Mata ta dalilin yin auren wuri.