Saudiyya Ta Hana ‘Yan Najeriya Bizar Umrah

images

Dubban ‘yan Najeriya da ke da niyyar tafiya Umrah a wannan wata na Ramadana babu lallai burinsu ya cika saboda rashin biza daga kasar Saudiyya.

Wannan ya biyo bayan wani sabon tsarin bayarda biza da ƙasar ta Saudiyya ta fito da shi.

Kawo yanzu cikin waɗanda suka biya kuɗin tikiti da biza ya ɗuri ruwa.

Tuni ta bayyana ga masu jiragen sama cewa bana ba za su samu kasuwa kamar yadda suka saba yi ba.

Kazalika, masu masaukin baƙi da ke da ɗakunan haya na masu Umara da aikin Hajji za su samu nakasu a abin da za su samu.

Wata majiya ta shaida mana cewa akwai jirgin da ya kamata ya tashi da maniyyatan Umrah mutum kusan 300 amma bai tashi ba.

Watan Ramadana lokaci ne da dubban ‘yan Najeriya ke tafiya Umrah domin falalar da ke tattare da yin Umrah a lokacin Azumi.

Amma abin da ya tabbata shi ne, a bana da dama ba za su samu damar zuwa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply