Satar Tallafin CORONA Zalunci Ne – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar, ya siffanta wasoson kayan tallafin corona, sace-sace da lalata ma’aikatun gwamnati a matsayin zalunci da mugunta.

Sarkin wanda yayi jawabi a taron murnar cikar gidan tarihi na Arewa shekaru 50, ya jinjinawa matasan Arewa bisa biyayyan da suka yiwa shugabanni, wajen ?in shiga cikin wannan bahallatsar.

Ya ce talauci ba uzuri bane da zai sa a rika lalata dukiyoyin kasa. Yace: “Mun san akwai talauci amma talauci ba uzuri bane na yin mugunta.”
“Saboda abinda ya faru a kwanakin nan mugunta ne wasu bata gari sukayi kuma ina ganin akwai bukatar muyi Alla-wadai da hakan.”

Ya kalubalanci shugabannin Arewa suyi aiki wajen gina yankin domin wanzar da manufar marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Related posts

Leave a Comment