Satar Tallafin CORONA: Filato Ta Yi Asarar Naira Biliyan 75 – Lalong

Gwamnan Jihar Filato Mista Simon Bako Lalong, ya bayyana cewar Jihar ta yi asara na kimanin Naira Biliyan 75 a sace-sacen da ɓatagari suka yi ranar Asabar da Lahadi sakamakon zanga-zangar #EndSARS.

An ruwaito yadda wasu ɓatagari a jihar suka fasa rumbunan abinci domin neman kayan tallafin Korona, amma wasu suka koma satan kayayyakin mutane da sunan Ganima.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a hira da matasan jihar kan abubuwan da suka faru a gidan gwamnatin jihar dake Rayfield Jos.

“Rahotannin da na samu daga masana shine abubuwan da akayi asara zasu kai bilyan 75 a yanzu.” “Wannan ci baya ne sosai saboda bamu da kudin maye abubuwan da aka lalata ko aka sace.” “Har yanzu bamu farfado daga illan da cutar COVID-19 tayi mana ba.”

“Mun kirga dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu 32 da aka kaiwa hari akayi sace-sace.”

Gwamnan ya kara da cewa ya san halin da matasan jihar ke ciki na rashin aikin yi da rayuwa mara dadi, inda ya yi kira ga matasan su guji yin duk wani abu da zai zama barazana ga zaman lafiya a jihar da Najeriya gaba daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply