Satar ?aruruwan ?alibai A Katsina: Buhari Ya Gaza Ya Wajaba Ya Yi Murabus – Shugaban Kare ‘Yancin Arewa

An yi kira da babbar murya ga mai girma Shugaban ?asa Buhari da cewar cikin gaggawa ya gaggauta yin murabus daga karagar mulki biyo bayan abin kunyar da ya faru a Jihar shi ta Katsina na satar ?aruruwan ?aliban Makaranta alhali yana jihar a wannan lokaci.

Shugaban Kungiyar kare ‘yancin Arewa Alhaji Kamaluddin Nasiru Nasiha ya yi wannan kiran, a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna dangane da irin halin koma baya da harkar tsaro ke fuskanta a yankin Arewa.

Shugaban ?ungiyar ya ?ara da cewar ko shakka babu Buhari ya tozarta kuri’un jama’ar Arewa wa?anda suka fito ?wai da ?war?wata suka za?e shi bisa ga kyakkyawar fata da zato da suke dashi a gareshi, amma abin ba?in ciki da takaici abubuwa gaba ?aya sun lalace ya zamana gwamma jiya da yau.

Kamaluddin Nasiru Nasiha yace a yau an wayi gari yankin Arewacin Najeriya ya zama tamkar ma?abarta, saboda wanzuwar ta?ar?arewar tsaro, bin hanyoyin Kaduna zuwa Abuja ko Zariya zuwa Funtuwa ko Faskari sun gagari matafiya saboda matsalar tsaro, babu shakka wannan gazawa ce ga wannan gwamnati kuma lallai yin murabus ?in Shugaban ?asa shine mafita.

Daga ?arshe Shugaban kare ‘yancin Arewan ya yi kira ga Buhari da ya yi gaggawar sallamar Shugabannin tsaro, ya maye gurbin su da wasu muddin ya zamana shi ba zai sauka ba, tura ta kai bango abin ya isa haka!!!.

Related posts

Leave a Comment