Sarautar Kano: Babban Alkali Ya Gayyaci Alkalan Da Suka Bada Umarni Masu Cin Karo Da Juna

FB IMG 1716698490096

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Alkalin Alkalai na Ƙasa (CJN), Mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya gayyaci babban alkalin babbar kotun tarayya, da kuma babban alkalin babbar kotun jihar Kano kan wasu hukunce-hukuncen wucin gadi da suka bayar a masarautar Kano.

Umarnin da ke cin karo da juna ya haifar da rashin tabbas da rudani a jihar.

Tun da fari, babbar Kotun Tarayya da ke Kano, karkashin Mai Shari’a S. A. Amobeda ce ta bayar da umarnin korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga fadar Kofar Kudu, tare da karfafa ikon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

A daya hannun kuma, Mai shari’a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin hana hukumar ‘yan sanda, DSS tsare Sarki Muhammadu Sanusi II.

Yanzu dai al’ummar jihar Kano na ci gaba da zama cikin ɗar-ɗar tun bayan da gwamnatin Kano ta yi sabuwar dokar da ta rushe masarautu da gwamnatin da ta gabata ta kafa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply