Mai martaba Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa ganin damar Allah ya ba shi mulki ba don ya fi wani ba, haka kuma cikin ganin damarsa ne ya karbi abinsa. Hakan ya fito ne daga bakin sarkin lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Ta’awun Bainad Du’a Ahlussunnah ta Jihar Kaduna Karkashin jagorancin Sheikh Abba Adam Koki a masaukinsa da ke Kano.
In ba a manta ba tsohon sarkin ya sauka a Kaduna ne shekaranjiya Lahadi domin saukaka wa masoyansa da ke so su zo Legas su gaishe shi kamar yadda ya bayyana a ganawarsa da ‘yan jarida lokacin da ya ziyarci Gwamna El-Rufai. Sarkin ya bayyana wa malaman da suka kawo masa ziyara cewa ya karbi duk hukuncin da Allah ya yi saboda mulki na Allah ne ya ba wanda ya so, ya kuma karba a lokacin da ya so. “Ganin daman Allah ne ya ba mu mulki, kuma cikin ganin damarsa ne ya karbi mulkisa. Wannan dalilin ne ya sa ni da iyalina tun lokacin da abin da ya faru, ya faru muka ci gaba da.
“Alhamdulillah mun sami albarkar tashi da malamai tun daga gida Sarki Halifa da su Alkali Umar da Alkali Malam Kuliya har zuwa zama da ku da ‘yan uwa irinsu Malam Bashir Aliyu. Kuma duk wanda ya zauna da ku, da yardan Allah in dai ba an haramta masa ba, tilas ya samu abubuwan da zai amfana da su a rayuwarsa. Wadannan abubuwa da aka fada, shi Alku’ani sai a ga kamar yau aka saukar da shi. Da za a samu wata aya da ta yi magana a kan wani abu, da za a canza suna sai a ga kamar da wannan mutumin ake magana”
Sarki Sanusi ya ce ba abin da zai ce wa Allah sai godiya a halin da ya tsinci kansa, “Kullum muna gode wa Allah, shi ya sa tun da muka bar Kano mu ba mu ma tsaya mun yi magana a kai ba saboda duk abin da zai faru indai ana bin Alku’ani an san abin da zai biyo baya Insha Allahu. San da Ubangiji ya ce, “Kulillahu Malikal Mulk”. Ai a wannan ayar abu hudu ya fada. Yana bayar da mulki, yana karban mulki. Shi ke daukakawa, shi ke kaskantarwa. Kuma zai iya hada wa mutum mulki da daukaka ko mulki da kaskanci. Kuma zai iya ba ka daukakar ba mulkin da kuma kaskancin ba mulkin. To ita daukakar ita Allah ya ce a nema. Daukaka ake nema ba mulki ba. Shi ya sa in Allah ya ba da ita sai a gode masa domin shi yake ba wanda ya ga dama. Ba wani abin da muka yi wa Allah. Ba mu da labarin Allah ya fi son mu a kan wani. Ganin damarsa ne saboda kullum shi ake gode wa tunda duk abin da aka gani na daukaka daga wurinsa yake, said ai mu ci gaba da addu’a Allah ya ci gaba da daukaka mu da duk na tare da mu.
”Kamar yadda ake fada, “sarauta rai ne da ita” in lokacin ta ya zo na karba, dole ka sauka. Duk wanda ya ce ya cire ka a sarauta fada yake yi kawai. Saboda in Allah bai yarda ba bai isa ya cire ka ba. Amma daga ranar da Allah ya ba mutum iko ya ce ya cire ka, daman ranar ne Allah rubuta za ka bar wurin kuma in ma ba ka daga ba, za a fita da gawarka. Duk wanda yake karatu, yake nazari ya san wannan. Saboda haka ita sarauta ba a cewa Allah ya karba, sai dai a ce Allah ya bayar. Cikin zuri’ar Dabo mutum dubu nawa ne? a cikin mutum dubban nan cikin shekara 200, ni ne na 12 cikin dubbai da suka gaji wannan sarautar. Bai ba wa mahaifina na, har ya mutu bai yi ba kuma dan sarki ne. Bai taba ba wani jika ba duk sai ‘ya’ya. Ni ya fara ba w ajika, sannan ya ba mu dama iya kokari muka sauke nauyin amanar da ya daura mana. Mun shekara kusan shida in ban da mu gode wa Allah me za mu ce masa. Duk in aka ce za a yi fushi ma, an yi wa Allah butulci. Da Allah bai bayar ba fa, wa zai yi zancen karba? Kuma da da ya bayar bayan wata daya ya karbi ranka fa? Kuma lokacin karban, da da ya tashi karba ranka ya karba fa? Da yanzu ba ma a yi da kai balle ka yi bakin ciki. Amma Allah ya bar ka da ranka da lafiyarka da iyalinka da kuma ba a san me ya rubuta maka a gaba ba, saboda haka ba abin da za mu ce ma Allah sai godiya da farin ciki da ya ba mu dama duk inda muke mu ci gaba da bauta wa al’umma” inji Sarki Sanusi.
A jawabinsa, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana wa sarkin cewa, wannan majalisa wanda Sheikh Abba Adam Koki ke jagoranta ta Ta’awun Bainad Du’a Ahlussunnah ta Jihar reshen Jihar Kano ta zo ne ta gaishe da Maimartaba sarki da kuma jaddada goyon baya da kuma yi masa addu’a bisa iftila’I da ya shafe su su jama’ar Kano ba shi kadai ba, da kuma sake yin addu’a gare shi a kan Allah ya ci gaba da tallafa masa, ya ci gaba da ba shi goyon baya.
Shehin malamin ya kara da cewa, sannan sun zo ne su kara ba shi hakuri a kana bin da ya faru na yanayin da aka samu kai a Kano wanda an san wani abu ne da ya faru wanda ba a saba ganin irinsa ba.
A karshe tsohon sarkin ya gode wa jama’an Kano da kasa baki daya na irin kaunar da aka nuna masa. “Muna godiya ga mutanen Kano da na kasar nan baki daya na irin kauna da suke nuna mana, kuma mu ma zuciyarmu tana tare da su”