Mai girma, Sarauniyar Ingila ta turo sakon taya murna ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai da za’ayi yau ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.
Mai bai wa Shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata takardar da ya bayar ranar Laraba a Abuja.
Kamar yadda sakon yazo, “Ina mai matukar farin cikin taya Najeriya cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai, ina kuma yiwa Najeriya fatan alheri da fatan wanzuwar farinciki da cigaba.”
A wani labari na daban, daga cikin shagulgulan cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yancin kai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a Abuja, ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2020.
An sanar da hakan a wata takarda da mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa akan yada labarai, Femi Adesina ya sa hannu. Shugaban kasa zai yi jawabin ne bayan anyi faretin zagayowar shekarar.