Sarakuna Sun Goyi Bayan Mata Masu Ya?i Da Covid 19

An bayyana kokarin da gamayyar kungiyoyin Mata masu yaki da cutar Covid 19 a Jihar Kaduna ke yi a matsayin abin da ya dace kuma abin yabawa wanda zai taimaka wajen shawo kan matsalar cutar ta Covid 19.

Mai girma Bunun Zazzau Hakimin Doka Kaduna Alhaji Balarabe Muhammad Tijjani ya yi wannan yabon, lokacin da yake kar?ar bakuncin tawagar ?ungiyar Matan a fadar shi dake Kaduna.

Bunun Zazzau ya ?ara da cewar ko shakka babu wannan cuta ta Covid 19 ta yi illa sosai a tsakanin jama’a, kuma rashin samun ilimi da wayar da kan al’umma ya taimaka wajen dagula al’amurra.
“Amma a halin yanzu sakamakon samun wadannan kungiyoyi naku abin zai taimaka wajen shawo kan matsalar.

Tun farko da take gabatar da jawabi Jagorar gamayyar kungiyoyin Matan Dr. Lydia Umar ta bayyana cewar ma?asudin ziyarar ta su fadar Hakimin shine domin neman goyon bayan sarakuna a matsayin su na iyaye wajen aiwatar da ayyukan kungiyar.

“Muna da kyakkyawar fahimtar cewa Sarakuna za su taimaka wajen fadakar da jama’a tasirin ayyukan kungiyar tasu, wannan ya sanya muke neman alfarma a wajen su domin samun nasara”.

Dr. Umar ta Kara da cewar nan gaba kadan ?ungiyar tasu za su ?addamar da ayyukan nasu a hukumance, kuma tana fatan wannan kudirin sai zama wani tubali na kai wa ga nasara.

Related posts

Leave a Comment