Sarakuna Biyu A Kano: Gwamna Abba Ya Bada Umarnin Kama Tsohon Sarki Aminu Bayero

IMG 20240525 WA0097

Rikicin sarauta a Kano ya dauki sabon salo bayan da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke daga kujerar Sarkin Kano kwanaki biyu da suka wuce, ya koma birnin Kanon a ranar Juma’a da daddare.

Aminu Ado Bayero tare da rakiyar wadansu magoya bayansa ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke birnin inda bayanai suka nuna cewa ya koma Kano ne domin ya shiga cikin gidan sarki bisa la’akari da cewa maganar cire shi na gaban kuliya.

Sai dai gwamnatin jihar Kano da ta samu bayanai cewa Aminu Ado Bayero zai koma Kanon sai gwamna Abba Kabir Yusuf da wadansu kusoshin gwamnati suka yi maza da misalin karfe daya na dare a ranar Juma’a suka yi wa Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu rakiya zuwa cikin fadar Sarkin Kano.

Kuma bayanai sun ce Sarki Muhammadu Sanusi da wadansu jamii’an gwamnati a cikin fadar sarkin Kano suka kwana.

Sai dai a halin yanzu, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umurni ga jami’an tsaro su kama sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero saboda jawo zaman dardar a cikin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ta ce gwamnan a matsayinsa na babban mai tsaro a jihar ya umurci kwamishinan ‘yan sanda ya kama sarkin da aka tubewa rawani ba tare da bata lokaci ba saboda ‘kokarin jawo rikici’ a cikin jihar.

A ranar Alhamis ne dai majalisar dokokin Kano ta rushe masarautun Kano guda biyar da suka haɗa da Kanon da Bichi da Karaye da Gaya da Rano waɗanda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙira.

A ranar ne kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarki na masarautar Kano ɗaya tilo.

A jiya Juma’a ne gwamnan ya miƙa wa sabon sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki, inda kuma sabon sarkin aka ce zai ci gaba da zama a gidan gwamnati har zuwa lokacin da yanayi zai bayu na shiga gidan sarautar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply