Sanatocin Kudanci Sun Sabunta Kungiyar Su

IMG 20240310 WA0183

Kwana guda bayan zazzafar muhawara a majalisar dattawa da ta haddasa dakatar da sanata Abdul Ningi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin Najeriya – sanatocin kudancin kasar sun farfaɗo da ƙungiyarsu tare da zaɓar shugabanni.

Ƙungiyar sanatocin kudancin ƙasar ta zaɓi sanata, Adetokunbo Abiru mai wakiltar Legas ta gabas a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

A baya dai shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ƙasar, Senator Opeyemi Bamidele ne ke jagorantar ƙungiyar.

Sanatoci 51 ne daga jihohin kudancin ƙasar 17 suka taro domin farfado da ƙungiyar, wata tara bayan ƙaddamar da majalisar ta 10.

Sanata Bamidele ya ce ƙungiyar ba sabuwa ba ce domin kuwa tana nan tun lokacin majalisa ta tara, yana mai cewa ayyukan ƙungiyar sun dakata ne sakamakon samun sabon muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar da ya samu.

Hakan na zuwa ne kwana guda da Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun ‘zubar da ƙimar majalisar.’

Labarai Makamanta

Leave a Reply