Sanatocin Arewa Sun Zabi ‘Yar’adua A Matsayin Sabon Shugaba

images 2024 03 15T085937.429

Kungiyar Sanatocin arewacin Najeriya ta nada Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya a zauren majalisar dattawan kasar a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Yar’Adua, wanda dan jam’iyyar APC ne – ya zama sabon shugaban kungiyar kwanaki biyu bayan saukar Sanata Abdul Ahmed Ningi – wanda dan jam’iyyar hamayya ta PDP ne – daga shugabancin kungiyar bayan da majalisar ta dakatar da shi wata uku.

Sanata Ningi, wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar, ya zargi gwamnatin kasar da yin cushen naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin kasar.

Haka kuma kungiyar sanatocin arewacin kasar ta kuma nada Sanata Tahir Munguno daga jihar Borno a matsayin mai magana da yawun kungiyar.

Sanata Munguno -wanda dan jam’iyyar APC ne – ya maye gurbin Sanata Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP daga jihar Kano.

Labarai Makamanta

Leave a Reply