Sanata Kyari Ya Maye Gurbin Abdullahi Adamu A Shugabancin APC


Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa bayan kwashe shekara daya da ‘yan watanni yana jagorantar jam’iyyar.

Sabon shugaban riƙo na jam’iyyar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbabar da murabus din Adamu kwana guda bayan kafafen yada labarai a Najeriya suka wallafa labarin cewa rashin jituwa tsakanin Sanata Adamu da shugaba Tinubu ya tursasa masa yar da ƙwallon mangwaro

Shugaban jam’iyyar ta APC ya bar mukamin ne kimanin wata biyar bayan ya jagorance ta a zaben shugaban kasar, inda ta yi nasara.

Bayanai sun ce Adamu ya ajiye aikin ne tare da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore.

Akwai dai alamu na cewa an dinga samun takun-saka a cikin jam’iyyar tun bayan da shugaba Tinubu ya kama mulki, kimanin watanni biyu da suka gabata.

Ajiye muƙamin shugaban jam’iyyar zai iya alamta cewa akwai wani babban rikici ne tsakanin ƴaƴan jam’iyyar da aka kasa samun masllaha.

A lokacin da ya sanar da ajiye muƙamin na Abdullahi Adamu, shugaban riƙon jam’iyyar na ƙasa, Abubakar Kyari ya ce Sanata Adamu bai bayyana dalilin ajiye muƙamin nasa ba.

Kwamitin gudanarwa na APC din a zamansa na ranar Litinin ne ya amince da naɗa Sanata Abubakar Kyari wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar a ɓangare arewacin Najeriya a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar.

A watan Maris ɗin 2022 ne aka zaɓi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa bayan gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi shugaban riƙo na kusan shekaru biyu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply