Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar gwamnatin Jihar ta sake bude makarantu 45 cikin 75 da ta rufe a fadin jihar saboda matsalar tsaro.
Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi a jihar, Kabiru Attahiru na ya bayyana matakin lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin gaggawa kan ilimi a jihar a ofishinsa.
Attahiru ya ce gwamnati da jami’an tsaro na aiki tukuru domin tabbatar da cewa tsaro ya inganta a jihar.
”Muna sa ran kyautatuwar yanayin tsaro a Zamfara domin ganin mun bude sauran makarantu 30 da suka rage a rufe”, in ji Attahiru.
Gwamnatin Jihar Zamfara dai ta rufe makarantu a watan Satumban 2021 bayan garkuwa da daliban makarantar sakandaren Kaya da ke karamar hukumar Maradun.