Sama Jannati: Saudiyya Za Ta Tura Mace Ta Farko Sararin Samaniya

Hukumar kula da sararin samaniya ta Saudiyya ta ?addamar da shirin sama jannati a karon farko da ya ha?a da aika mace ta farko ?ar ?asar zuwa sararin samaniya a 2023.

Shirin zai mayar da hankali ne wajen horar da ?wararru ?an asalin Saudiyya don su yi tafiya mai nisan zango da mai gajeren zango a jirgin sama jannati zuwa sarrain samaniyar.

Shirin zai bai wa ?an sama jannati Saudiyya damar aiwatar da binciken kimiyya don ci gaban ?an adam a ?angarorin da suka fi muhimmanci kamar lafiya da ci gaba mai ?orewa da kuma fasahar sararin samaniya.Shirin Sama Jannatin na Saudiyya, wanda yana daga cikin burukan da masarutar ke son cimma a shekarar 2030, zai aika ?an sama jannatin ?asar don kyautata rayuwar mutane.

?aya daga cikin ?an sama jannatin mace ce ?ar asalin Saudiyyan, wadda tafiyarta za ta zama wani abu na tarihi da ba a ta?a gani ba a masarutar.A watanni masu zuwa Saudiyya za ta ?addamar da tsare-tsarenta na zuwa sararin samaniya, da suka ha?a da shirin yi wa al’umma hidima daga can.

Related posts

Leave a Comment