Sama Da Yara Miliyan 10 Za Su Fa?a Matsananciyar Yunwa A 2021 – UNICEF

Majalisar dinkin Duniya ta fitar da wani ruhoton cewar za a samu adadin sama da yara milyan 10.4 a kasashe 7 ciki harda Nijeriya za su yi fama da matsananciyar cutar yunwa a shekarar 2021.

A cikin kasashen da matsalar za ta shafa sun hada da; Congo, Nijeriya, Burkina Faso, Mali, Niger, Sudan, South Sudan da kuma kasar Yemen.

UNICEF ya ce rashin tsaro da ake fama da shi a Jamhuriyar Demokdiyyar Congo, matsin tattalin arziki, yaduwar cutar corona da kuma matsin rayuwa zai jefa yara miliyan 3.3 mafiya yawansu ‘yan kasa da shekara 5 cikin cutar ta yunwa a shekara mai kamawa.

A Arewa maso gabashin Nijeriya kuwa, yara sama da 800,000 ne ake tsammanin za su fuskanci wannan matsala ta yunwa, inda akalla 300,000 a cikinsu za su kasance a halin gargarar mutuwa.

Sakamakon binciken na UNICEF ya nuna cewa yara miliyan 1.4 za su yi fama da cutar yunwar a shekara mai kamawa a Sudan ta Kudu sakamakon rikicin dake wakana, rashin tsaro, karancin magani, ruwa da ingantaccen yanayi.

A Burkina Faso, Mali da Niger adadin yaran da suke fama da cutar ta yunwa zai karu da kaso 21% zuwa milyan 2.9 saboda rashin zaman lafiya, gudun hijira da kuma sauyin yanayi a wadannan yankunan.

Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa sama da yara milyan 2 ne ke fama da cutar ta yunwa a kasar Yemen kuma ana tsammanin karuwar adadin a cikin shekarar 2021.

Tunda fari dai Asusun na UNICEF ya bukaci gudunmawar Dala bilyan 1 daga masu bada tallafi don ci gaba da tallafawa yara a kasashen dake fuskantar irin wannan matsalolin a sabuwar shekarar.

Related posts

Leave a Comment