Rahoto na musamman da wata kungiya mai bin diddigin matsalar tsaro a Afrika ta fitar na nuna cewa sama da ‘yan ?ungiyar Boko Haram 4,000 ne su ka yi watsi da kungiyar, suka kama gabansu, su ka bar sansanonin ta’addanci a kasashen Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru.
Rahoton wanda Kungiyar Bin Diddigin Matsalar Tsaro a Afrika, mai suna ISS ta fitar kwanan nan, dangane da halin da tsaro ke fuskanta a nahiyar Afirka.
Wannan adadi ya nuna an samu matukar raguwar manyan kwamandoji da sauran karabitin mayakan Boko Haram a cikin kasashen hudu.
Rahoton wanda ISS ta fitar ya na kunshe ne a cikin shafuka 28, wanda ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram sama da 2400 su ka zubar da makamai a Chadi, 1000 a Najeriya, 584 a Kamaru, sai kuma 243 a Nijar.
ISS ta bayyana cewa dalilai da yawa ne su ka sa masu ta’addancin har sama da 4,000 su ka watsar da makaman na su.
Dalilan sun hada cewa, wasu ‘yan Boko Haram din ba don akida su ka shiga ba, kama su aka yi da karfin tsiya aka saka su cikin ta’addanci, bayan an yi garkuwa da su.
Sannan kuma akwai dalili na matsin lambar da su ke fuskanta, saboda yawan hare-haren da sojojin hadin-guiwa na MJTF ke kai masu a Yankin Tafkin Chadi.
Wannan ya sa rayuwar su ta shiga cikin hatsari, babu sakewa ko kadan.
Da yawan wadanda su ka shiga domin akida sun dawo daga mummunar akidar, sun gane ba tafarkin tsira ba ne.
Rahoton ya nuna akwai tsatstsauran hukunci ga masu karya doka a cikin sansanonin Boko Haram. Fasikanci da sata abu ne mai gamuwa da kakkarfan hukuncin da ke kara tsoratar da wasu da dama, musamman ganin yadda ake aiwatar da hukuncin.
Sannan kuma akwai rashin jituwa da kuma adawa tsakanin bangarorin masu ta’addanci. Sai kuma dalilan saduda da daidaikun ‘yan ta’adda ke yi, su na gajiya da kasancewa cikin rayuwar kunci a cikin dazuka.
Wata Jami’ar Bincike a ISS mai suna Teniola Tayo, ta bayyana cewa adadin gaskiya ne, kuma gwamnatocin kasashen hudu sun yi na’am da rahoton.
Shi ma Malik Samuel na ISS ya bayyana cewa ba shaci-fadi su ka yi wajen tattara adadin har na sama da Boko Haram 4,000 ba.
“A Najeriya mun samu adadin ne da ‘Operation Safe Heaven’, cibiyar ta ke kula da tubabbun ‘yan Boko Haram da kuma yi masu wankin kwakwalar kankare masu akidar ta’addanci.