Sama Da Mutum 400 Aka Sace A Borno Ba 200 Ba – AMNESTY

IMG 20240229 WA0096

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewa iƙiraarin da Kungiyar Ƙungiyar Afuwa ta Duniya, ‘Amnesty International’ ta yi a ranar Juma’a, ta tabbatar da cewa sama da mutane 400 yara da manya masu gudun hijira ne Boko Haram suka arce da su, ba 200 ba, kamar yadda rahotonnin farko su ka bayyana.

An sace su ne daga sansanin gudun hijira daban-daban, a Gamboru Ngala, Jihar Barno a cikin wannan makon.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya tabbatar da sace masu gudun hijirar, amma bai bayyana adadin yawan su ba.

Amnesty International dai ta ce ɗaruruwan waɗanda aka sacen sun fito ne daga Babban Sansani, Zulum, Sansanin Arabic duk a yankin Gamboru.

A ranar Alhamis Gwamna Babagana Zulum ya ce gwamnati ba ta tantance yawan adadin waɗanda aka arce da su ɗin ba, kamar yadda jaridar HumAngle ya ruwaito.

An sace mutanen da suka haɗa da mata da ƙananan su 400, rana ɗaya da ɗaliban firamare da na sakandare 287 da aka sace a Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

“Sace mutanen nan da Boko Haram suka yi a baya-bayan nan, hakan ya nuna ƙarara cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da gwamnatin sa ba su da wani kyakkyawan shirin magance wannan gagarimar matsalar tsaro.”

Yayin da AI ta yi Allah wadai da wannan garkuwa da mutum sama da 600, ta kuma ce hakan ya nuna yadda Boko Haram suka sake darkakowa da ƙarfin su.

Ƙungiyar ta ce gwamnati na ci gaba da nuna cewa gagarimin aikin kare lafiya, dukiyoyi da rayukan jama’a ba ya gaban wannan kwamiti.

Haka kuma ƙungiyar ta Afuwa ta Duniya ta ce ya kamata a riƙa ɗora laifin it n wannan ɓarna a kan kwamandojin da tsaron yankin da abin ya faru a duk lokacin da aka kai farmaki a yankin da suke tsaro.

Wannan gagarimar garkuwa da mutane a Kaduna da Barno, ta zo ne kwana biyu kacal bayan Ministan Tsaro Muhammad Badaru ya fito fili ya bayyana cewa rashin isassun sojoji ne ke sa mahara da ‘yan bindiga yawan kai hare-hare kwanan nan a wasu sannan Najeriya, musamman a Arewa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply