Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sama Da Kashi 64 Na ‘Yan Najeriya Za Su Fuskanci Barazanar Yunwa – Majalisar Dinkin Duniya

IMG 20240225 WA0030

Majalisar Dinkin Duniya ta yi garga?in cewar ‘yan Najeriya miliyan 82 – kimanin kashi 64 na ‘yan ?asar – ka iya fuskantar matsalar yunwa nan da shekarar 2030.

Haka kuma Majalisar ta yi kira da gwamnatin ?asar ta magance matsalar sauyin yanayi da matsalar ?wari da sauran abubuwan da yi wa harkar noma barazana.

Jaridun Najeriya sun ambato jami’in Majalisar Dinkin Duniyar, Taofiq Braimoh – wanda ya wakilci kodinetan ayyukan jin ?ai na hukumar abinci da ayyukan noma na majalisar – na bayyana haka lokacin da yake jawabi kan matsalolar ?arancin abinci a taron ?addamar da shirin bun?asa ayyukan noma na ‘CropWatch’ a birnin Abuja.

Mista Braimoh ya ce akwai bu?atar gwamnatin Najeriya ta ?auki matakan da suka dace cikin gaggawa don magance matsalar.

“Gwamnatin Najeriya tare da ha?in gwiwa masu ruwa da tsaki, sun gudanar da bincike na shekara-shekara da suka saba gudanarwa kan abinci. Sakamakon binciken ya tayar da hankali, kimanin mutum miliyan 82 ne za su fuskanci yunwa nan da 2030,” kamar yadda Jaridun ?asar suka ambato Braimoh na bayyanawa.

Ya ci gaba da cewa matsalar rashin abinci da ?asar ke fama da shi, baya rasa nasaba da matsalar sauyin yanayi da duniya ke fama da ita, da matsalar ?wari da wasu abubuwa da ke yi wa harkar noma barazana a ?asar.

Hasashen na Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne a daidai lokacin da ?asar ke fama da matsalar tsadar abinci, lamarin da ya tilasta wa gidaje da dama ha?ura da sayen abincin da suka saba ci.

A cikin rahotonta baya-bayan nan, hukumar ?ididdigar ?asar ta ce farashin abinci a ?asar ya ?aru zuwa kashi 40.66 a watan Mayu, matakin da aka jima ba a ga irinsa ba.

Exit mobile version