Sallah: Dalilinmu Na Bijire Wa Umarnin Sarkin Musulmi – Sheikh Lukwa

Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Malamin musulunci da ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da sallar Idi a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, Sheikh Musa Lukwa, ya kare kansa kan abun da ya aikata.

Sarkin Musulmi ya sanar da cewar ba a ga jinjirin watar Shawwal na1443AH ba a ranar Asabar, amma Sheikh Lukwa ya ce matsayar Sultan din ba daidai bane.

“Wani Malami a jami’ar Danfodio, Dr. Maigari, ma ya tabbatar da ganin jinjirin watan a jami’ar kuma akwai rahotanni kan ganin jinjirin watan daga kimanin garuruwa 10 a Jega, jihar Kebbi, wanda babban limamin Jega, Malam Bashar ya tabbatar.

“Kuma Sheikh Dahiru Bauchi ma ya tabbatar da ganin jinjirin watan a wurare da dama a kasar. “Don haka mun yi sallar idinmu daidai da koyarwar Annabin tsira wanda ya bukace mu da mu yi azumi sannan mu sha ruwa da zaran an ga jinjirin wata.

An yarda cewa dole musulmi ya bi shugabanninmu musamman ma Sultan amma bisa sharadin cewa bai saba ma Allah da Manzonsa ba, inji Sheikh Lukwa

“Ba zai yiwu ka zantar da hukunci bisa hujjar kimiyya ba saboda ya sabawa addininmu kuma shi kansa Imam Malik ya yi hani ga hakan.”

Kan ko sun sanar da abun da suka lura ga kwamitin neman wata, Sheikh Lukwa ya ce babu amfanin aikata haka saboda sun rigada sun yanke shawara da zuciyarsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply