Sakin Mayakan Boko Haram 101 Ya Haifar Da Cece-Kuce

Akalla mayakan Boko haram 101 ne ake zargi an saka daga gidan yarin Kirikiri dake Ikeja babban birnin Jihar Legas.

An ruwaito wani shafin yanar gizo na gidauniyar binciken kwakwaf, na cewa sakin mayakan na daga cikin wata yarjejeniyar sakin sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda aka kama tun ranar 28 ga watan Maris.

Wasu majiyoyi sun ce wadanda aka sakin na cikin mutanen da ke jiran shari’a tun shekarar 2009, kuma suna da masaniyar harin gidan yarin Kuje tun kafin aukuwarsa.

Majiyar ta ce ”sun saki mayakan Boko Haram 101 a asirce, da safiyar ranar Asabar. An kwashe watanni ana kulla yarjejeniyar sakinsu”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply