?ungiyar Miyetti Allah MACBAN ta karyata cewa ta shiga cikin tattaunawa da ‘yan bindiga wajen sakin daliban makarantar sakandare gwamnatin GGSS Kankara, a jihar Katsina wanda wasu ‘yan Bindiga suka sace.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar Laraba, ya ce gwamnatin ta tuntubi Miyetti Allah domin tattaunawa da ‘yan bindiga kan sakin dalibai da aka sace a makarantarsu.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyanawa Saturday Sun a hirar wayan tarho cewa bai da masaniya kan abinda Masari ke magana a kai.
A cewarsa, “sai dai idan gwamnan da shiyyar kungiyarmu na Katsina yake nufi, amma ba uwar kungiya ta kasa ba.”
Daga baya, Ngelzarma, ya tattauna da shugabannin Miyetti Allah na Katsina, kuma sun musanta rahoton cewa gwamnatin jihar ta tuntubesu domin shiga tsakaninsu da yan bindiga domin sakin daliban makaranta.
Hakazalika, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre, Bello Abdullahi Bodejo, ya ce babu wanda ya tuntubesu ko ya tattauna da su kan lamarin.
Yace: “Bamu san ‘yan bindigan ba kuma bamu bukatan saninsu kuma bamu da wata alaka da su. Babu wani mamban Miyetti Allah Kautal Horee ko a kauyuka da ya san yan bindigan.”
Masari karya yake, ba damu aka tattauna da ‘yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba:
Mun kawo muku cewa a ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan.
A ranar Juma’a 11 ga wata ne ‘yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa’o’i kadan.