Sai Mun Cire Hassada Da Girman Kai Kafin Samun Zaman Lafiya A Arewa – Dingyaɗi

Ba Shakka Muddin Muna Son Ganin Ci gaba Da Zaman Lafiya A Arewarmu Sai Mun Debe Hassada, Kwadayi Da Girman Kai A Tsakanin Juna.

Cin Duga-dugan Juna Da Manyan Arewa Keyi Ba Abin Da Yake Haifarwa Illa Kiyayya Da Ganin Kyashi Da Tozarta Juna Tare Da Rarrabuwar Kawuna.

Arewa Ta Shiga Gararin Da Bata Taba Shiga Ciki Ba A Sakamakon Rashin Hadin Kai, Mutunta Juna Da Son Kai Na Wasu Dake Ganin Ala Dole In Ba Abin Da Suke So Ba; Sai Dai Kowa Ya Rasa.

Ba Ruwansu Da Neman Makoma Ta Gari Ga Arewa, Muddin Ba Nasu Ko Yadda Suke So Aka Bi Ko Akayi Ba.

Tumassanci, Cin Mutunci, Rashin Hakuri Da Tsoro Ba Shakka Mafarinsu Daga Kwadayi Da Son Kai Ne, Muddin Akwai Su A Zukatan Shugabaninmu, Dattawanmu Da Matasanmu, Hakika Arewa Sai Gyaran Allah.

Dan Arewa Ka Falka, Lokaci Nan Ba Na Girman Kai Ko Son Rai Bane; Hadin Kai Da Kishin Yankinmu Da Al’ummarmu Bisa Gaskiya, Amana Da Adalci Ne MAFITA!

YA Allah Ga Arewa, Kayi Mana Makoma Mai KYAU!!!

Yusuf Dingyadi,
Ya rubuto ne daga Sokoto

Labarai Makamanta