Sai Bayan Rantsuwa Kotu Za Ta Ci Gaba Da Shari’a Kan Nasarar Tinubu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun sauraron korafin zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zamanta zuwa 30 ga watan Mayu kan kalubalantar sakamakon zaɓen watan Fabrairu.

Hakan na nufin sai an rantsar da sabon shugaban ƙasar, Bola Tinubu, a ranar Litinin, 29 ga wata kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

Hakan ya biyo bayan kin amincewa da bukatar yaɗa hukuncin kotun ta talabijin da masu orafin suka shigar.

Hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar.

Kafin ta ɗage zaman nata a yau Talata, kotun ta haɗe ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyun adawa na PDP da Labour da APM ke yi game da nasarar Tinubu.

A ranar Litinin mai zuwa ne za a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.

Kotun sauraron ararrakin zaɓen da ta fara zama mako biyu da suka gabata, ta ce tana da wata uku don sauraron shaidu da kuma yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen.

‘Yan takarar adawa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour Party, na son a yi watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, inda suke zargin cewa an tafka maguɗi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply