Sai Arewa Ta Haɗa Kai Kafin Fita Daga Matsalar Da Take Ciki- Saira

Ina Kira Ga ‘Yan Uwana ‘Yan Arewa Da Mu Hada Kai Domin Shawo Kan Matsalolin Da Suka Addabi Yankunanmu.

Fitaccen darakta a masa’antar shirya finafinan Hausa, Malam Aminu Saira, ya yi kira ga mutanen Arewa da su hada kansu domin shawo kan matsalolin da ke damun yankin.

Malam Aminu Saira, wanda ya bayyana hakan a shafin sa na facebook, ya ce “Kira gare mu Talakawan Arewa da Malaman mu, da Sarakunan mu, da Attajiran mu, da jami’an Gwamnatin mu, mu hada karfi wuri guda don ganin an kawo karshen wannan masifa da ta addabi yankin mu na Arewa. Allah ka karfafe mu, Allah kai mana dauki #EndNorthBanditry #EndBokoHaram”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply