Sai An Biya Miliyan 100 Kafin Mu Saki ‘Yan Matan Kwalejin Yawuri – ‘Yan Bindiga

Fitaccen ɗan ta’addan jihar Zamfara Dogo Gide da yayi garkuwa da dalibai mata ‘yan kwalejin Yawuri dake jihar Kebbi ya rantse ba zai saki sauran wadanda suka rage a hannunsa tare da malaman su har sai an kai masa diyyar naira miliyan 100 da ya bukata.

Wannan matsayi ya biyo bayan wani sautin hirar da aka nada tsakanin wani daga cikin mahaifin dalibar dake hannunsa da mahaifiyarsa wadda ta bukaci ya sake sauran wadanda yayi garkuwar da su.

Gide wanda yayi kaurin suna wajen kai munanan hare hare yana hallaka jama’a a Jihohin Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, yace muddin iyayen daliban na bukatar ganin sun kubuta, to dole sai sun biya wadanan kudade da ya gindaya.

Sautin da aka nada ya bayyana wata mata da akace itace mahaifiyar ‘dan ta’addan tana nuna damuwa akan ci gaba da garkuwa da daliban, musamman ganin kananan yara ne.

Mahaifiyar ta bayyana cewar bata zama da ‘dan nata a daji, amma ta ziyarce shi ne a wannan karo, kuma ba zata bar wurin da yake ba har sai an kammala tattaunawa tsakanin sa da iyayen daliban da aka tsare da su domin ganin sun kubuta.

An jiyo mahaifiyar dan ta’addan na cewa jama’a suyi hakuri da ɗan nata saboda yaranta ne ke dibarsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply