Sai An Biya Kuɗi Kafin A Sabunta Katin Ɗan Ƙasa – NIMC

Hukumar yin rajistar katin dan kasa NIMC ta ce daga yanzu za a rika biyan Naira dubu 15 ga duk wanda yake son ya gyara shekaru haihuwarsa a katinsa na dan kasa ko NIN.

Hukumar ta kuma ce duk wanda yake da bukatar a sake masa sabon katin dan kasa ko NIN a sakamakon bacewa ko lalacewa to zai biya Naira 5,000.

Shugaban shiyya na hukumar NIMC, Fummi Opesanwo, wanda ke fadin haka yau Laraba a Lagos ya ce duk wanda kuma yake so a gyara masa adreshinsa ko sunansa dake katinaa na NIN to zai biya Naira 500.

Hukumar ta ce duka kudaden zasu shiga asusun Gwamnati ne saboda haka “Yin rajistar NIN kyauta ne amma za a caji kudi kamar ga duk wanda ke son gyara bayanansa kamar yadda na fada a dub 15 gyara shekaru, 5000 kuma wanda ke son sabunta katinsa sannan 500 ga masu gyara adreshinsu ko sunayensu saboda haka a kiyaye ga dalilin da yasa ake karba kudi a wajen yin NIN din kuma asusun Gwamnati kudin ke zuwa”

Daga ranar 19 ga watan Fabrairu ne dai NIMC ta ce wa’adin da aka ɗebar wa ƴan Nigeria na yin rijistar zai ƙare, a yayin da kuma ranar 19 ga wannan wata na Janairu shi ne wa’adin da aka ɗebar wa waɗanda suka riga suka yi rijistar ya zamana sun laƙana lambobinsu da na wayoyin salularsu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply