Fittacen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, yace zai je har fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin neman yafiyar sa akan ba ta masa suna da makiyan sa keyi ta shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai, kuma zai je wajen shugaban ne a madadin talakawan Nijeriya.
Rarara ya ce, gwamnatin APC na kokari matukar gaske, wajen ganin ta samar da cigaba, saidai kuma cutar korona bairos ta kawo mata cikas, kuma zai yi waka mai suna ‘’Kainuwa” wacce zai bayyano ayyukan shugaban kasa guda 192, kuma talakawan Nijeriya ne za su dauki nauyin wakar, saboda haka kowa yana iya bada nasa tallafin daga kan N1,000 zuwa sama, ta hanyar tura masa a asusun ajiyarsa na banki.
‘’Zan nemi ganin shugaban kasa, na ce masa, talakawa suna kara baka hakuri da wannan zage-zagen, kuma masu kaunarsa har yanzu suna kaunarka, saboda kudi baya canja su, kuma duk mai zagin shugaban kasa ‘yan jawota ne, ko kuma ‘yan rubuta ka tura ko kuma ‘yan shaci fadi, zan tattaro ayyukan shugaban kasa guda 192, wanda idan na fada, duk talaka mai kaunar Buhari zuciyar sa za ta yi fari, kuma talakawan da suka zabi Buhari sune za su bani kudi na yi wannan wakar.” cewar mawaki Rarara.