Sace Dalibai: Shugaban Tashoshin ‘Yanci Ya Jajanta Wa Gwamna Da Iyayen Yara

images 2024 03 10T071301.511

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Tijjani Ramalan Shugaban Tashocin ‘Yanci Na Liberty ya wa Gwabna Kaduna Sanata Uba Sani da Iyayen Yara Jaje sace ɗalibai 287 a Kaduna

Ramalan ya yi tir da garkuwa da ɗaliban sakandare 287 a garin Kurebe, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna da fatan Jami’an Tsaro kasa za su Gaggauta ceto su.

Shugaban tashoshin ‘yancin ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba wa manema labarai a Abuja.

“Abin takaici ne da baƙin ciki yadda matsalar tsaro ke cigaba da lalacewa a Najeriya musamman yankin arewa muna kira da babbar murya ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su yi dukkanin mai yiyuwa domin ceto yankin daga durkushewa”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply