?ungiyoyin ?asashen duniya na ci gaba da matsa wa hukumomin Najeriya lamba, don ceto ?aliban nan su kusan 50, da masu satar mutane suka yi awon gaba da su daga wata makarantar Sakandire ta Kagara a jihar Neja.
Da sanyin safiyar ranar Talata ne wasu ?an bindiga suka sace ?aliban da kuma wani malaminsu da iyalinsa shida mata da ‘ya’ya, a makarantar sakandiren garin Kagara da ke jihar Neja a arewacin Najeriya.
A wannan karon hukumar kula da ?ananan yara ta Majalisar ?inkin Duniya wato UNICEF ta ce tana cike da matu?ar tashin hankali a kan sace gomman ?aliban, da kuma yadda aka kwashe fiye da kwanaki uku ba tare da an ji wani batu mai gamsarwa dangane da shirin da ake yi na ceto su ba.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce abin takaici ne yadda ake samun hare-hare a makarantun ?ananan yara, duk da cewa ?ancinsu ne su nemi ilimi ba tare da wani shara?i ba.
Yadda ?an bindiga ‘suka kashe abokina suka tafi da ?an uwana ?alibai a GSS Kagara’
Sace-sacen ?alibai a makarantu hu?u da suka girgiza Najeriya
Illar bai wa masu satar mutane kudin fansa a Najeriya.
Ta kuma yi kira ga hukumomin Najeriya su tashi tsaye wajen tabbatar da kare makarantu musamman na kwana, ta yadda tsarin ilimi a Najeriya zai ci gaba da wanzuwa ba tare da wata barazana ba.
Amurka da wasu manyan ?asashen duniya, da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da sace ?aliban, tare da yin kiran sakinsu ba tare da ?ata wani lokaci ba.
Shi dai shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin ceto ?aliban a cikin aminci, tuni kuma ya tura tawagar wasu jami’an gwamnatinsa zuwa zuwa jihar ta Neja domin jagorantar ku?utar da su.
Wasu rahotanni da aka samu a ranar Alhamis, sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da maharan da suka sace wa?annan ?alibai.
Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa wasu tubabbun yan bindiga da kuma wasu jagororin Fulani ne ke jagorantar tattaunawar domin ganin an ku?utar da ?liban lami lafiya.
Wasu masana kan lamuran tsaro dai ga ganin cewa da alama mahukuntan Najeriya basu ?auki wani darasi daga abubuwan da suka faru a baya, na sace ?alibai a wasu makarantu da ke arewacin ?asar ba.