Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa an kai wa makarantar GSSS Kankara hari ne, musamman don a tozarta shugabancinsa.
Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Disamba yayin da yake gabatar da jawabi a kan ceto yaran da aka yi a gidan gwamnatin jihar Katsina.
Buhari ya bayyana farin cikinsa a kan ganin yadda aka ceto daliban ba tare da an cutar da wani ba. Kamar yadda Buhari yace ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, a kan yadda satar tazo daidai da ranar da ya isa Daura, garinsa na haihuwa.
Satar ?aliban da sakin su ya zama wani abu ba sa bamban ba, kuma manazarta al’amurra na cigaba da sharhi akai, inda ake ganin da akwai siyasa a cikin sace daliban.
An samu bayanai masu cin karo da juna akan yadda aka samu ceto yaran daga hannun ‘yan Bindiga, inda gwamnatin Jihar Katsina ke bayyana cewar an yi amfani da kungiyar Miyetti Allah ne wajen ceto yaran, a gefe guda kuma Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle na i?irarin cewa shi ya zanta da ‘yan Bindiga har aka sako yaran, yayin da ?angaren rundunar soji ke bayyana ita ta ceto yaran.