Shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘Yan Najeriya jawabin sabuwar shekara yau Juma’a anjima ?aya ga watan Janairun 2021.
Mai taimaka wa shugaban kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin ?arfe 7:00 na safe.
Malam Garba Shehu, ya bu?aci kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da su jona da gidan talabijin na ?asar wato NTA da kuma gidan rediyo na tarayya FRCN domin su ma su ya?a jawabin na shugaban kasar.
Sabuwar Shekara ta 2021 ta zo wa ‘yan Najeriya cikin wani yanayi da suke fuskantar matsi na talauci da kalubale na rashin tsaro musamman a yankin Arewacin Kasar.
Gwamnatin Buhari na shan suka a ciki da wajen ?asar akan abin da ake gani na gazawarta ta fuskar samar da tsaro ga ‘yan ?asa da gaza ceto jama’a daga ?angin talauci dake addabar su.