Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘Yan Najeriya jawabin sabuwar shekara yau Juma’a anjima ɗaya ga watan Janairun 2021.
Mai taimaka wa shugaban kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce shugaban zai yi jawabin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe.
Malam Garba Shehu, ya buƙaci kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da su jona da gidan talabijin na ƙasar wato NTA da kuma gidan rediyo na tarayya FRCN domin su ma su yaɗa jawabin na shugaban kasar.
Sabuwar Shekara ta 2021 ta zo wa ‘yan Najeriya cikin wani yanayi da suke fuskantar matsi na talauci da kalubale na rashin tsaro musamman a yankin Arewacin Kasar.
Gwamnatin Buhari na shan suka a ciki da wajen ƙasar akan abin da ake gani na gazawarta ta fuskar samar da tsaro ga ‘yan ƙasa da gaza ceto jama’a daga ƙangin talauci dake addabar su.