An yi kira da babbar murya ga shugabannin Jam’iyyar APC mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da cewa, suyi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin sun shawo kan matsala ta korafi da ‘ya’yan jam’iyyar ke yi na zargin ?oye katuttukan zama ?an jam’iyya da ake zargin wasu da yi.
Kiran ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar ta APC a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba Jakadan Hayin Banki, jim ka?an bayan kammala sabunta rijistar zama ?an jam’iyya da yayi a maza?ar shi dake Hayin Banki Kaduna.
Gambo Abba ya cigaba da cewar ko shakka babu jam’iyyar APC tana nan da farin jinin jama’a kamar yadda aka santa tun asali, ta la’akari da yadda jama’a ke tururuwa wajen sabunta rijistar zama ?an jam’iyya, sai dai babbar matsalar da ake fuskanta ita ce ?arancin katuttukan jam’iyyar, wanda hakan ke haifar da damuwa kuma ba ?aramar barazana bace ga jam’iyyar.
Jakadan Hayin Banki ya bu?aci Shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki su binciki zargin ?oye katuttukan da ake yi, domin akwai zargin cewa ana ?oye katuttukan ne domin wata manufa da ake son amfani da ita a lokacin za?ukan fidda gwani, inda wasu ke burin sai nasu ne kawai za su kai labari.
Gambo Abba wanda ya ta?a tsayawa takarar Kujerar ?an Majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar maza?ar Kawo a jam’iyyar APC a za?en da ya gabata, ya sha alwashin cigaba da bayar da dukkanin gudummuwar shi wajen ganin APC ta cigaba da samun tagomashi a matakin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa dama jiha baki ?aya.