A ranar Lahadi ne babban Shugaban Rundunar ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana siffofin sabbin jami’an rundunar SWAT da a ka kafa domin maye gurbin rundunar SARS da aka rushe.
Muhammad Adamu ya bayyana cewa za a fara baiwa sabbin jami’an SWAT horo daga ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, 2020. A cewar IGP Adamu, babu wani tsohon jami’in SARS da aka saka a sabuwar rundunar SWAT.
“Jami’an da aka zaba domin bada horon Matasa ne, zakakurai da ke da karfi a jika, sannan kuma sun shafe a kalla shekaru bakwai suna aiki da rundunar ‘yan sanda.
“Hakazalika jami’an da aka zaba ma su tsarki ne – ba a taba samunsu da laifi ba a baya, sannan kuma su na da lafiyar jiki da koshin lafiyar hankali domin jure duk wahalhalun da ke tattare da horon da za a basu.
“Za a yi wa dukkan jami’an sabuwar rundunar SWAT binciken koshin lafiyar jiki, gwajin tu’ammali da kayen maye da miyagun kwayoyi da sauransu. “Sai wanda ya haye dukkan wadannan gwaji ne zai samu shiga cikin jerin jami’an da za a bawa horo a sabuwar rundunar SWAT,” a cewar Shugaban ‘yan sandan.