Babban Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayyana cewa rundunar za ta bukaci naira biliyan 24.8 domin zuba wa ababen hawanta mai a duk shekara, domin sau?a?a wahalar zirga-zirga na jami’an su.
Shugaban ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a yayin kare kasafin kudin 2021 a gaban kwamitin ‘yan sanda na majalisar wakilai.
Muhammad Adamu ya bayyana cewa suna fuskantar tarnaki sakamakon rashin kebe masu isashen kaso a kasafin kudi, lamarin da ke haddasa tasgaro ga ayyukan Rundunar.
“Babbar matsalar ita ce abinda aka ware mana ba zai ishe mu gudanar da ayyukan mu tsawon shekara guda ba. “Idan ka dauki misali, man fetur da ababen hawanmu ke sha a kulla-yaumin, motocinmu kan sha mai na kimanin naira biliyan 22.5 a cikin shekara kawai.
“Idan ka hada lissafin, a man fetur kawai an kusan karar da abinda aka ware mana, ba a ma zo ga bangaren gyare-gyare ba. Idan muna son kula da ababen hawanmu, muna bukatar akalla sama da naira biliyan takwas a shekara daya.”
Shugaban ‘yan sandan ya ce a kudin da aka ware musu a kasafin 2021 na Naira biliyan 469.4 an zaftare shi zuwa Naira biliyan 44.6.