Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Manyan Hafsoshi Ritaya

Labarin dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ?asa na bayyana cewar Rundunar Sojojin Najeriya ta yi wa wasu Janar-janar har 12 ritaya.

An yi wa wa?anda aka yi wa ritayar faretin bankwana a Cibiyar Horas da Zaratan Sojoji ta Jaji, ranar Juma’a, a Kaduna.

Wa?anda aka yi wa ritayar sun ha?a da Manjo Janar shida, Burgediya Janar biyu da kuma wasu manyan hafsoshi biyu.

Manjo Janar ?in da aka yi wa ritaya ?in sun ha?a da Lamidi Adeosun, I. Birigini, C.M Abraham, E.C.C Agundu, T.O.B Ademola, A.M Jalingo da A.S Maikobi.

Burgediya Janar biyu da aka yi wa ritaya kuma sun ha?a da M.A Bashrudden da Dam Onayiveta.

Akwai kuma sauran hafsoshi biyu da su ma ritayar ta shafe su.

Da ya ke jawabi a wurin faretin wanda aka shirya a taron laluben makamar inganta tsaron ?asa na kwanaki hu?u da aka shirya a Jaji, Kaduna, Adeosun ya yi godiya da bankwana a matsayin kan sa da sauran wa?anda aka yi wa ritayar.

Ya gode wa Allah da ya yi masu tsawoncin rai har su ka kawo ranar da ritayar su ta zo daga aikin soja.

Ya yi kira ga na baya su ci gaba daga inda su su da suka tafi suka tsaya.

Sannan kuma ya gode wa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Farouk Yahaya da shi da Kwamandan Jaji, Manjo Janar Victor Ezugwu.

Related posts

Leave a Comment