Rundunar Soji Za Ta Binciki Kisan Fararen Hula Bisa Kuskure Da Jami’anta Suka Yi

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Hafsan Sojan Sama Air Marshal Oladayo Amoa ya ce rundunar ta kafa wani kwamiti da zai tattaro bayanai kan dukkan lamuran kai hari bisa kuskure kan fararen hula da sojojin saman kasar suka yi.

A cewarsa kwamitin wanda ya kunshi manyan jami’an rundunar zai yi bitar abubuwan da suka faru har aka kai ga faruwar hakan domin daukar matakan magance su.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, Air Marshal Amao ya sanar da hakan ne a yau Alhamis, yayin da yake bude taron karawa-juna-sani kan aikace-aikacen rundunar sojin saman na shekara ta 2022 da ke gudana yanzu haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa-Ibom.

A cewarsa manufar hakan ita ce samun shawarwari kan muhimman matakan da ya kamata a dauka domin rage yawan kashewa da raunata fararen hula a kasar yayin wasu aikace-aikacen da rundunar ta sojin sama ke yi a wasu sannan kasar.

Air Marshal Amao ya kuma kara da cewa binciken yana kuma da manufar kara tabbatar ana bin Kadin yadda sojojin rundunar ke aiwatar da umarnin da aka ba su da ba rundunar ta NAF damar koyon wasu muhimman darussan kan yadda za ta kaucewa faruwar hakan a gaba ko kuma rage irin ta’adin da irin wannan kuskure ke yi.

Kazalika da kuma daukar karin matakai don rage cutar da fararen da ke zaune a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

Yayin da yake taya sabbin matasan matukan jiragen yaƙi 17 da aka yaye a wajen taron, Mista Amao ya hore da su bi ka’idojin aiki da aka shimfida a yayin da suke fagen daga, kana su dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen kare fararen hula da kuma rage illata su.

Sai dai sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ba ta sanar da lokacin da ake tsammanin kammala wannan binciken da fitar da sakamako ba.

Mutuwa da kuma raunata fararen-hula a cikin hare-haren sojojin sama a Najeriya abu ne da ke ta maimaituwa a shekarun bayan bayan nan, tun bayan sakin wani bam bisa kuskure da suka yi a garin Rann na jihar Borno wannan ya yi sanadin mutuwar ‘yan gudun hijira da ma’aikatan agaji fiye da dari daya shekaru biyar da suka wuce.

Ko a watan Satumban bara ma fararen hula fiye da 10 ne suka rasa rayukansu a kauyen Buhari na jihar Yobe wasu kuma 20 suka samu raunuka a wani harin da wani jirgin saman soji ya kai musu bisa kuskure.

Lamarin dai bai tsaya kan fararen hula ba kadai domin wasu sojoji da dama sun rasa rayukansu a wata Afrilun barar lokacin da wani jirgin yaƙi ya kai wa motar su hari bisa kuskure a yankin Mainok na jihar Borno bayan da sojojin na kasa suka kira a kawo musu dauki a arangamar da suke yi da mayakan Boko Haram a lokacin.

Akwai lamurra makamantan haka da suka faru a wasu yankuna cikin har da jihar Zamfara inda sojojin ke fada da ‘yan fashin daji.

Labarai Makamanta

Leave a Reply