Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin kubutar da fiye da yara ‘yan makaranta 200 da ‘yan bindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.
Da yake zantawa da manema labarai game da ayyukan rundunar a makonni 2 da suka gabata, Daraktan Yada Labaran Ma’aikatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, yace Rundunar Sojin Najeriya ta kudiri aniyar ceto dukkanin wadanda ‘yan bindiga ke garkuwa dasu cikin lumana.
Saidai a yayin wani taro daya gudana a ranar Alhamis, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ya zargi masu makarantu da gazawa wajen kai rahoton satar mutane cikin lokaci ga hukumomin tsaro.
Haka kuma, ya dora alhakin satar ‘yan gudun hijra na baya-bayan nan a garin Gamborun Ngala na jihar Borno akan bijirewar da suka yiwa umarnin da aka basu na kada su fita daga sansaninsu ba tare da sanin jami’an dake kula da wurin ba, inda suka fita neman itacen girki.
Sakamakon satar daliban, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro dasu kamo barayin tare da kubutar da daliban, inda ya jaddada cewar gwamnatinsa ba zata lamunci biyan kudin fansa ba.
8- Darajar Naira Ta Ƙara Faɗuwa Ƙasa Warwas – Babban Banki