Rundunar SARS Na Ƙuntatawa Talakawa – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar yayi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakin da ya dace kan rundunar SARS “inda ya ce an kafa ta ne domin yaki da manyan laifuka irinsu fashi da makami da satar mutane aka kafa hukumar ba wai kuntatawa talakawan najeriya ba.

Wannan ya biyo bayan rahotannin da wasu daga cikin jaridun kasar suka wallafa, da kuma wani hoton bidiyo da ya nuna wasu da ake zargin jami’an rundunar SARS ne sun kashe wani mutum tare da guduwa da motarsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba a kofar wani Otel da ke kira Wetland, a garin Ughelli da ke Jihar Delta.

Cikin bidiyon an nuna jami’an da ake zargi sun dauki motar mutumin da suka kashe kirar Lexus SUV.

Ba wannan ne karo na farko da ake samun takun saƙa tsakanin ƴan Najeriya da rundunar SARS kan irin ayyukan da rundunar ke yi, waɗanda mutane ke zargin cewa zalunci ne zalla.

An dade ana zargin jami’an SARS da take hakkin bil’adama a fadin kasar yayin da su kuma a nasu bangaren suke karyata zargin.

Kuna goyon bayan barin ayyukan jami’an SARS ko kuwa kawai a dakatar da aikin nasu a kawo wani tsarin na daban?

Labarai Makamanta

Leave a Reply