Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ruftawar Kasa Ta Hallaka Yara Takwas A Jihar Kebbi

IMG 20240421 WA0047

Shugaban ?aramar hukumar Hon. Muhammad Dahiru Ambursa, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara shirye-shiryen yi wa yaran jana’iza.

Ya kuma ce akwai wasu ?arin yara biyu da suka jikkata ciki har da wanda ya karye a ?afa.

To sai dai wani mutum da abin ya faru a gaban idonsa ya shaida wa BBC cewa yara tara ne suka rasu, lokacin iftila’in da ya faru da safiyar ranar Asabar

Shugaban karamar hukumar ya ce mafi yawa daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su almajirai ne wa?anda ke aikin ha?ar ?asar gini a yankin.

Honarabul Ambursa ya ce ya bayar da umarnin dakatar da ha?ar ?asar gini a wurin.

”Mun bayar da umarnin killace wurin da waya tare da saka alamar da ke nuna cewa an hana ha?ar ?asar gini a wurin, mun kuma bu?aci hakimai da sauran iyayen ?asa da su saka a yi shela, don hana mutane ha?ar ?asar gini a wannan wuri”, in ji shi.

Masu ?aramin ?arfi dai kan yi amfani da ?asa wajen yin bulon ?asa da za su yi amfani da shi wajen yin gine-ginen musamman a garuruwa da ?auyuka a Najeriya.

Exit mobile version