Shugaban ƙaramar hukumar Hon. Muhammad Dahiru Ambursa, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara shirye-shiryen yi wa yaran jana’iza.
Ya kuma ce akwai wasu ƙarin yara biyu da suka jikkata ciki har da wanda ya karye a ƙafa.
To sai dai wani mutum da abin ya faru a gaban idonsa ya shaida wa BBC cewa yara tara ne suka rasu, lokacin iftila’in da ya faru da safiyar ranar Asabar
Shugaban karamar hukumar ya ce mafi yawa daga cikin yaran da lamarin ya rutsa da su almajirai ne waɗanda ke aikin haƙar ƙasar gini a yankin.
Honarabul Ambursa ya ce ya bayar da umarnin dakatar da haƙar ƙasar gini a wurin.
”Mun bayar da umarnin killace wurin da waya tare da saka alamar da ke nuna cewa an hana haƙar ƙasar gini a wurin, mun kuma buƙaci hakimai da sauran iyayen ƙasa da su saka a yi shela, don hana mutane haƙar ƙasar gini a wannan wuri”, in ji shi.
Masu ƙaramin ƙarfi dai kan yi amfani da ƙasa wajen yin bulon ƙasa da za su yi amfani da shi wajen yin gine-ginen musamman a garuruwa da ƙauyuka a Najeriya.