Ronaldo Zai Koma Wasa Manchester United

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya Cristiano Ronaldo ya aika wani sakon bankwana na musamman ga magoya bayan kungiyar Juventus, yayin da ya koma Manchester United.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘dan wasa Cristiano Ronaldo ya aika wannan sako ne a shafinsa na Instagram, ya na mai gode wa duk magoya bayan Juventus.

Da yake sallama Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ya bada duk karfinsa ga kungiyar Italiyan a lokacin da yake dauke da rigar su na shekaru uku. A bankwanan da ya yi a ranar 27 ga watan Agusta, 2021, Ronaldo yace ba zai taba manta wa da Juventus ba domin kungiyar ta bar tambari a cikin zuciyarsa.

“A yau na bar wannan kulob mai ban-kaye, kungiyar da ta fi kowace a kasar Italiya, daya daga cikin manyan kungiyoyin da ke kaf Turai.”

“Na bada zuciyata da rai na a lokacin da na ke Juventus, kuma har na tashi, ina kaunar birnin Turai.” Goal.com ta rahoto CR7 yana cewa “tiffosi bianconeri” sun girmama shi, ya yi kokarin saka wa ta maida hankali a kowane wasa, a kowace kaka, a kowane gasa.

“Zan cigaba da zama daga cikinku. Yanzu kun shiga tarihi na; ina ji cewa na shiga cikin na ku. Italiya, Juventus, tiffosi bianconeri, Turin, za ku kasance a zuciyata.” Ya zaman Ronaldo a Seria A.

‘Dan kwallon na Portugal mai shekara 36 a Duniya ya ji dadin soyayyar da aka nuna masa a Turin, inda ya lashe gasar Seria A sau biyu da Copa Italiya a 2020.

Labarai Makamanta

Leave a Reply