Mai Shari’a Aisha Adamu Aliyu ta babbar kotun Jihar Kano ta umarci kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kar?e ragamar mulki tare da fitar da sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Umarnin na kotu ya nuna cewa, “An bayar da umarnin wucin gadi na hana mutane biyar da ake ?ara da duk wani mai ala?a da su, su daina gabatar da kansu a matsayin sarakunan Kano, Bichi, Gaya, Rano da Karaye har zuwa lokacin da za a saurari ?arar da aka shiga a gaban kotu.
“An bai wa kwamishinan ’yan sandan Kano umarnin gaggauta kar?e ragamar fadar Sarki da ke kan titin zuwa gidan gwamnati tare da fitar da wanda ake ?ara daga fadar.
Kotun ta dage sauraren ?arar zuwa ranar 11 ga watan Yunin 2024.
Wa?anda ake ?arar sun ha?a da sarakunan Kano Karaye, Gaya, Bichi da Rano, da aka tube da kuma, shugaban ’yan sanda, daraktan DSS, NSCDC da Sojoji.
Wa?anda suka shigar da ?arar su ne Babban Lauyan Jihar Kano, Shugaban Majalisar Dokokin Kano da Majalisar Dokokin Jihar.
Aminiya ta ruwaito cewar Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Isah Dederi ya shaida wa BBC cewar gwamnatin jihar ta ?arbi umarnin kotu na dakatar da tsige Aminu Ado Bayero tare da dawo da Sarki Sanusi II a ranar Litinin.