Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce neman da ake yi shugaban jam’iyyar, Dr Iyorchia Ayu, ya yi murabus, ba lokacin da ya kamata bane kuma ba zai haifar da alheri ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a hirarsa da Muryar Amurka (VOA), Hausa a birnin Washington DC, a ranar juma’a.
Atiku ya ce bai goyi bayan cire Ayu ba a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa saboda, hakan ba dabara bane mai kyau kuma abubuwa za su sake dagulewa ne maimakon su gyaru.
“Ba daidai ba ne a wannan lokacin mu yi tunanin sauya shugaban jam’iyyarmu, yayin da muke daf da shiga zabe.”