Gwamnatin Jihar Bauchi ta gargadi mai martaba Sarkin Misau, Alhaji Ahmed Sulaiman daya bada hakuri a rubuce, kan sakaci da aikinsa na jagorancin al’ummar masarautar, inda hakan ya jawo salwantar rayuka 11 a rikichin manoma da makiyaya a kwanan baya.
Wan nan gargadi ta fito ne a wata takarda da gwamnatin ta fitar ta hannu babban mai tallafawa gwamnan Bauchin kan harkokin watsa labarai a ranar Asabar, kwamrade Mukhtar Gidado
Indai ba a manta ba tun lokacin da rikicin ya barke, bayan gwamnati ta kafa kwamitin binciken, tare da dakatar da Sarkin daga karagar Mulki, tare da shugaban karamar hukumar misau dawasu jigajigai a yankin, nan take kwamitin suka tsunduma cikin binciko musabbabin rikicin tare da bankado masu hannu a cikin tashin hakalin.
Biyo bayan mika sakamakon binciken ne gwamnatin ta fitar da matakin da ta dauka, tare da jan kunnen masu hannu a ciki dumu dumu, tare da cewa gwamnati baza ta sa ido tana bari a bata mata zamn lafiyar dake wanzuwa a jihar, shiyasa suka dauki wan nan matakin don yan’baya su kula.
Har ila yau, takarda ta ci gaba da cewa “Gwamnatin Bauchi ta yarda da dokkanin shawarar da kwamitin binciken ta bayar domim kar hakan ya sake aukuwa, cewa Sarkin Misau Alh. Ahmed Sulaiman ya bada gamsasshen hakuri ma gwamnati, tare da masarautar sa, da fatan baza a sake samun rikici filin kiwon makiyaya ba a yankin”.
Bugu da kari shawarar da kwamitin ta bayar a cikin takardar cewa dole Hakimin garin Chiroma Alh Ahmadun Amadu ya cigaba da zama na dakatarwa har sai an tabbatar da kammala binciken gaba daya
Takardar tace in har aka same shi da laifi, to zai rasa kujerarsa da mikashi hannun jami an tsaro domin tuhumarsa, kana sanarwar ta bama masauratar ummarnin tsige Ibrahim Yusuf Atiku daga kujerar sa na Wakilin Zadawa, kauyen da rikicin ya barke tare da mai unguwan garin.
Hakan nan ta ba da ummurni ma, babban kwamishinan shari’a na jihar da ya hada kai da kwamishinan yan’sanda na jihar, su kama Ibrahim Yusuf Atiku domin aikata al’mundahana da raba filayen dajin da kuma karbar kudade a hannun mutane ba bisa kaida ba.
“Masauratar misau ta tabbatar da ganin Ibrahim Yusuf Atiku bai sake hawa wata kujerar mulki ba ta mulki a nan gaba, ko da kujerar ta zama babo kuwa akanta”, takardar ta fada.
Haka nan “Darekta admin da Janaral Sabisis Malam Sule Abba da Shugaban inganta noma da ma’adinai Malam Baba Waziri, da kuma shugaban ma’aikata Aminu Abdullahi Disina dukkansu a karamar hukumar da suyi murabus na dole daga aikin gwamnati” ta fada.
A karshe gwamnatin ta amince da zurfafa bincike kan wadansu da ake zargin suna da hannu su goma sha shida, da ruruta wutar fitinan da tayi sanadiyan asaran rayuka da dumbin dukiya.
Tun a watan bakwai na wan nan shekarar ne 2020 gwamnati ta dakatar dashi Sarkin Misau da wasu masu fada aji, kan wan nan rikici da ya barke a kauyen Malunje cikin yankin Zadawa, a karamar hukumar Misau.
#