Rikicin Mali: Buhari Na Ganawa Da Shugabannin ECOWAS

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa tare da sauran shuwagabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) a yau Alhamis.

Ganawar tana gudana ne ta kafar yanar gizo, kamar yadda shafin fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter. Shuwagabannin ECOWAS, suna wannan ganawar ne a ci gaba da neman hanyoyin dai daita rikicin siyasa da ya barke a kasar Mali, wanda ya kai ga anyi juyin mulki a ranar Talata.

” A shafinsa na Twitter, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rikicin Mali ya jawo koma baya ga diflomasiyya a Afrika. Ya yi nuni da cewa, lokaci ya yi da sojojin mulkin mallakar kasar Mali su mika wuya tare da mayar da gwamnati a hannun farar hula, don wanzar da tsaro da zaman lafiya. Shugaban kasar ya ce Nigeria na goyon bayan shugaban ECOWAS, Shugaba Mahamadou Issoufou, a shawarwarin da ya kawo da zasu dai daita lamura a Mali, musamman na tuntubar AU da UN wajen sa hannu a lamarin.

“Zaman lafiya a siyasance a Mali, tamkar zaman lafiya ne a kasashen Afrika ta Yamma. Dole mu hada hannu, ECOWAS, AU, da UN wajen dai daita lamura, da mayar da mulki hannun farar hula.”

A ranar Laraba ne ECOWAS ta fitar da sanarwar dakatar da kasar Mali daga cikin ayyukan kungiyar tare da umurtar kasashen dake kungiyar su rufe iyakokin kasashensu da Mali. A ranar Talata, sojojin hamayya suka cafke shugaban kasa Keita da Firam Minista Boubou Cisse, bayan makonni na tashin hankali a kasar da ya fara daga ranar 10 ga watan Yuli. Rikicin siyasar ya kai ga gudanar da zanga zanga da ta haddasa jami’an tsaro suka kashe da yawa daga cikin masu zanga zangar. Sai dai Keita, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya yi murabus daga kujerarsa ta shugaban kasar Mali a ranar Laraba, domin gujewa zubar da jini a kasar. A cikin wata sanarwa, ECOWAS ta bukaci duk mambobinta dasu rufe iyakokinsu da Mali, ba shiga ba fita. Juyin mulkin da aka yi a ranar Talata, ya faru ne jim kadan bayan da tsohon shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya fice daga kasar, bayan neman sulhu da ya je.

Labarai Makamanta

Leave a Reply