Rikicin Kudancin Kaduna: El Rufa’i Ya Gargaɗi Sarakunan Yankin

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya kalubalanci ma su rike da sarautar gargajiya a kudancin jihar a kan su nuna wani wuri da aka kwace a yankunansu tare da mikawa wasu mutane ko kungiyoyi ba bisa ka’ida ba.

Kazalika, El-Rufa’i ya kalubalanci sarakunan su ba hukumomi da jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kudancin jihar Kaduna. Ya zaburar dasu a kan su zama ma su adalci ga duk jama’ar da ke zaune a karkashin masarautunsu.

El-Rufa’i ya yi wadannan kalamai ne a matsayin martani a kan zargin cewa wasu mutane sun kwace wasu sassan kudancin jihar Kaduna mai fama da yawaitar hare – hare a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Gwamnan ya fadi hakan ne ranar Talata yayin ganawarsa da majalisar sarakunan jihar, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki duk mazaunin yanki a matsayin kowane dan jiha zai iya zama kamar yadda kundin mulki ya amince.

Ya jaddada cewa yada labaran karya a kan gaskiyar halin da kudancin Kaduna ke ciki ba zai kashe gwuiwar gwamnatinsa a kokarinta na kawo karshen rikicin da aka shafe kusan shekara 40 ana fama da shi.

El-Rufa’i ya bayyana bakin cikinsa a kan yadda ake yada labarin karya a kan kwace gonaki da filayen jama’ar kudancn Kaduna. Ya ce an fara amfani da wannan labarin karya a lokacin da rikici ya taba barkewa a yankin a shekarar 2016/2017.

Labarai Makamanta

Leave a Reply